AHKAMUL JANA'IZ (Hukunce-hukuncen da suka shafi gawa)


WAJIBIN MARA LAFIYA

1.  Lallai mara lafiya ya yarda da hukuncin Allah, ya yi haƙuri da ƙaddarar da ta same shi, kuma ya kyautata zato ga Allah.
2. Ya kamata ya kasance tsakanin fata da tsoro, yana tsoron azabar Allah saboda zunubansa, kuma yana fatan rahamar ubangijinsa.
3. Duk inda cuta ya kai da tsanani, ba ya halatta (mutum) ya yi burin mutuwa, idan ya zama dole sai ya yi, to sai ya ce "Ya Allah ka raya ni idan rayuwa ta fi mun alheri, ka kashe ni idan mutuwa ta fi mun alheri".
4. Idan akwai haƙƙoƙin wasu a hannunsa, ya mayar da su ga masu su idan ya samu ikon hakan, idan bai samu ba sai ya yi wasiyya da hakan, saboda umarnin Annabi (SAW) a kan hakan.
5. Irin wannan wasiyyar ana so a gaggauta ta.
6. Wajibi ne ya yi wasiyya ga makusantansa wadanda ba su da gadonsa.
7. Ya halatta ya yi wasiyya da ƙimanin ɗaya bisa ukun dukiyarsa, ba ya halatta ya yi ƙari a kan haka, bal ma abun da ya fi falala shi ne ya yi cikin ƙasa da hakan.
8. Ya shaidanta mutum biyu musulmai adilai a kan wasiyyarsa, idan bai same su ba to ya shaidanta daga cikin waɗanda ba musulmai ba, kuma za a nemi su yi rantsuwa idan aka yi kokwanton shaidarsu.
9. Wasiyya ga iyaye da makusanta waɗanda za su ci gadon mai wasiyyar ba ta halatta, saboda an shafe wannan hukuncin.
10. Haramun ne a nufi cutarwa da wasiyya, kamar mutum ya yi wasiyya cewa a hana wasu cikin magadansa gadonsa, ko ya fifita wasu a kan wasu.
11. Wasiyya kan saɓon Allah batacciya ce, shari'a ba ta karɓanta.
12. A irin wannan zamanin da ƙirƙire-ƙirƙire cikin addini ya yi galaba a cikin mutane, musamman cikin abun da ya shafi Jana'iza, ya zama wajibi musulmi ya yi wasiyya cewa a yi wa gawarsa shiri da binnewa irin wanda musulunci ya tanada.

LAƘƘANA WA WANDA ZAI MUTU KALMAR SHAHADA

13. Idan Mutuwa ta zo wa mutum, akwai abubuwan da suke wajaba a kan waɗanda suke tare da shi:
a. Su laƙƙana masa kalmar shahada. 
b. Su masa addu'a. 
c. Kada su faɗi komai a gabansa sai alheri. 
14. Ana laƙƙana wa mai mutuwa kalmar shahada ne ta hanyar umartarsa ya faɗa, ba a dinga furta masa kalmar shahadar ba kamar yadda wasu suke zato. 
15. Game da karanta suratu yasin a wajen mamaci, ko juya fuskarsa zuwa alƙibka, babu hadisin da ya inganta a kan wannan.
16. Babu laifi musulmi ya halarci mutuwar kafiri, don ya bijiro masa da musulunci da fatan ya musulunta.

ABUN DA YAKE KAN WAƊANDA SUKA SHAIDA/HALARCI MUTUWAR WANI

17. Idan mutum ya mutu, rai ya fita, to akwai abubuwa da suka wajaba a kansu.
a. Su rufe idanuwansa.
b. Su masa addu'a.
c. Su lulluɓe shi da ƙyallen da zai suturce dukkan jikinsa.
d. Wanda ya mutu cikin ihirami, ba a rufe masa kai da fuska.
e. Su gaggauta shirya gawarsa da fitar da shi idan mutuwar ta tabbata.
f. Su binne shi a cikin garin da ya mutu, kada su fitar da shi zuwa wani garin, don hakan yana kore gaggauta binnewar da aka yi umarni.
e. Su yi gaggawar biya masa bashi daga cikin dukiyarsa, ko da kuwa ba shin zai shanye dukiyar da ya bari gabaɗaya, idan ba shi da dukiya yana kan gwamnati ta biya masa, idan ba ta aikata ba kuma in wani ya taimaka ya biya masa hakan ya yi.
ABUN DA YAKE HALATTA A YI WA GAWAR MAMACI.
18 Yana halatta a buɗe fuskar mamaci a sumbace shi, saboda Abubakar (R.A) ya sumbaci gawar manzon Allah (SAW), kuma ya halatta a masa kuka tsawon kwana uku.

WAJIBIN MAKUSANTAN MAMACI

19. Abu biyu suna wajaba a kan makusantan mamaci yayin da labarin mutuwarsa ta zo musu:
a. Haƙuri da yarda da hukuncin Ubangiji.
b. Faɗan "Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un" da ƙarin "Allahumma ajirni fi musibati wa akhlifni khairan minha".
20. Idan mace ta ƙi yin ado gaba ɗaya (saboda mutuwar wani nata), hakan ba ya cin karo da haƙuri muddin bai wuce na kwana uku ba, sai dai idan mijinta ne za ta yi takaba tsawon wata huɗu da kwana goma.
21. Sai dai idan bata yi wa wanin mijinta takaba ba saboda daɗaɗawa mijin da samun cikan biyan buƙatarsa da ita, to shi ne ya fi, kuma ana musu fatan Alheri mai yawa a bayan haka.

ABUN DA AKA HARAMTA WA MAKUSANTAN MAMACI

22. Annabi (SAW) ya haramta wasu al'amura, amma wasu mutane basu gushe ba suna aikata su idan aka yi musu mutuwa, wajibi ne a san waɗannan abubuwan don a nisance su:
a. Kukan kera.
b. Marin kai. 
c. Keta tufafi.
d. Aske gashi.
e. Barbaza gashi.
f. Cika gemu da wasu mutane suke yi na ƴan kwanaki saboda nuna baƙin ciki a kan mutuwa, idan kwanakin suka shuɗe sai su koma su ci gaba da askewa, wannan cikawan da suke kamar baza gashi ne, kamar yadda yake a bayyane, ƙari da kuma cewa bidi'a ne. Tare da sanin cewa yin kwalliya da aske gemu da da yawa cikin mutane suke yi saɓon Allah ne a fili bisa haɗuwar limaman mazhabobi huɗu, saboda saɓawar hakan ga dalilai masu yawa na shari'a.
g. Shelanta mutuwa a hasomiyoyi, saboda shi ma yana cikin shelanta mutuwa (An-na'ayu) da Annabi (SAW) ya yi hani da shi.

SHELANTA MUTUWA WANDA YA HALATTA

23. Yana halatta a shelanta mutuwa idan ba'a haɗa shi da abun da ya yi kama da shelantawa irin ta jahiliyya ba, hakan ma yana iya wajaba idan mamacin ba shi da wanda zai masa wanka da likkafani da salla. 
24. An so ga mai ba da labarin mutuwar ya nemi mutane da su nema wa mamacin gafara. Cewa da mutane suke yi a yanzu: "a karanta wa ruhin wane fatiha", ya saɓa wa sunnar da aka ambata, kuma babu shakka bidi'a ne, musamman ma saboda karatun ba ya kai wa ga mamacin a bisa zance mafi inganci.

ALAMOMIN KYAKKYAWAR CIKAWA

25. Allah mai hikima ya sanya wasu alamu bayyanannu da ake nuni da su a kan kyakkyawar cikawa, ya rubuta mana su cikin falalarsa da kyautarsa, duk mutumin da ya mutu da ɗaya daga cikinsu, suna kasancewa bushara a gare shi, madalla da wannan busharar.
1. Furta kalmar shahada yayin mutuwa.
2. Mutuwa da gumin goshi.
3. Mutuwa a daren Juma'a ko yininta.
4. Yin shahada a filin yaƙi.
5. Mutuwa a hanyar zuwa jihadi.
6. Mutuwa dalilin annoba.
7. Mutuwa dalilin ciwon ciki.
8. Mutuwa dalilin nutsewa a ruwa.
9. Mutuwa dalilin rusowar gini.
10. Mutuwar mace yayin nakuda.
11. Konewa a wuta.
12. Mutuwa a dalilin cutar kumburin huhu (pleuritis).
13. Mutuwa a dalilin tarin cutar fuka 
14. Mutuwar mutum a dalilin kare dukiyarsa.
15. Mutuwar mutum a dalilin kare Addininsa.
16. Mutuwar mutum a dalilin kare ransa.
17. Mutuwa yayin ba da kariya ga iyakokin kasar musulmi.
18. Mutuwa a cikin wani aiki nagari.
19.   Wanda azzalumin shugaba ya kashe saboda ya masa nasiha.

YABON MUTANE GA MAMACI

26. Idan a ƙalla musulmai biyu masu nagarta da ilimi cikin maƙotan mamaci da suka san shi, suka yabe shi da alkhairi, wannan yana wajabta masa Aljanna.
27. Idan mutuwar wani ta dace da lokacin zazzaɓin rana ko wata, hakan ba ya nuni a kan komai, kuma kudurce cewa yana nuni a kan girman wanda ya mutu yana cikin irin ƙrairayin jahiliyya da Annabi (SAW) ya yi inkarinsu a ranar da ɗansa Ibrahim ya rasu.

WANKE MAMACI

28. Idan aka samu mamaci, wajibi ne ga wasu cikin mutane su gaggauta wanke shi.
29. A wajen wanke mamaci za a kula da abubuwa kamar haka:
1. Wanke shi saɓi uku ko fiye da haka.
2. Adadin wankan ya zama mara.
3. Amfani da magarya wajen wankin ko madadinsa.
4. A saɓin karshe za a sanya masa turare, amma sanya kafur shi ya fi.
5. Warware kitso da wanke shi da kyau.
6. Taje gashi.
7. Kitsa kan mata tufka uku a kwantar da su baya.
8. Fara wankin da gaɓɓan dama, da wuraren Alwala.
9. Maza su wanke maza, mata su wanke mata, illa a inda aka kebance wanda bayaninsa zai zo.
10. Idan an cire wa mamaci tufafi za a yi mai wanka, a samu wani abu a suturce al’aurarsa.   
11. Ana rufe al’aurar ne don kar a gani ko a taɓa.
12. Wanda ya mutu a cikin ihrami ba a sa masa turare.
13. Ya halatta miji ya yi wa matarsa wanka ko ita ta mai.
14. Wanda ya fi sannin yadda wankan yake a sunna shi ya dace ya wanke gawa, musamman idan makusancinsa ne.

30. Wanda ya wanke gawa yana da lada mai yawa idan ya cika sharuda biyu:
1. Ya suturta duk wani abun ki ko aibu da ya gani tare da gawar kar ya fada wa kowa.
2. Ya tsarkake niyya ya nemi yardar Allah da wankan kar ya nemi wani abu na duniya da shi.

31. Ana so wanda ya wanke gawa shi ma ya yi wanka.
32. Ba a wanke wanda ya yi shahada a filin yaki ko da kuwa an tabbatar ya mutu da janaba.

YI WA GAWA LIKAFANI

33. Annabi (SAW) ya yi umarni idan an gama wanke gawa a sa masa likafani.
34. Ana sayan likafani daga dukiyar mamaci ko da iya dukiyar da ya bari kenan.
35. Ana so likafanin ya zama mai tsayi da faɗi yadda zai rufe dukkan jikinsa.
36. Idan ba’a samu damar siyan wanda zai rufe shi dukka ba sai a rufe daga kansa, inda ya saura kuma sai a rufe shi da ciyawar izkir ko wata ciyawar.
37. Idan mamata suna da yawa kuma likafani ya yi karanci, ya halatta a sanya mutane da yawa a likafani daya, sai a gabatar da wanda ya fi su sanin Alkur’ani ya fuskanci alƙibla.
38. Ba ya halatta a cire wa wanda ya yi shahada tufafi, ana binne shi da tufafinsa.
39. Ana so a ƙara wa shahidi likafani ko da ƙyalle ɗaya ne kari a kan tufafinsa.
40. Wanda ya mutu a cikin Ihrami ana rufe shi da tufafinsa da ya mutu da su.
41. Ana so likafani ya samu wadannan sifofin:
1. Ya zama fari.
2. A yi amfani da ƙyalle uku.
3. Ɗaya daga ciki ya zama yadin auduga mai ado.
4. A sa masa turare sau uku. 

42. Ba ya halatta a sayi likafani mai tsada ko a yi amfani da sama da kyalle uku.
43. Babu bambanci tsakanin likafanin namiji da na mace.

ƊAUKAR GAWA DA RAKIYARTA

44. Wajibi ne ɗaukar gawa da bin ta zuwa maƙabarta, yana daga cikin haƙƙin Musulmi mamaci a kan Musulmai.
45. Bin gawa iri biyu ne: 
1. Bin ta daga wajen Ahalinta zuwa inda za a mata salla.
2. Bin ta daga wajen Ahalinta har zuwa a binne ta, duka biyun Annabi (SAW) ya aikata.
 
46. Babu shakka cewa na biyun ya fi na farko lada. 
47. Bin gawa ya keɓanta da maza ne banda mata, saboda Annabi (SAW) ya hana mata bi, amma ba hani na haramci ba ne.
48. Ba ya halatta a raka gawa da abun da ya saɓa wa shari’a, nassi ya zo ƙarara a kan abu biyu, rusa kuka da bin ta da turare. 
49. Ɗaga murya ana zikiri a gaban gawa shi ma bai halatta ba, saboda bidi’a ne da kamanceceniya da kiristoci. 
50. Wajibi ne a yi sauri yayin kai gawa ba tare da an yi sassarfa ba.
51. Ya halatta mutum ya tafi a gaban gawar ko bayanta, da damanta da hagunta da kusa da ita, sai dai wanda yake kan abun hawa shi a baya zai tsaya.
52. Tafiya a gaban gawa da bayanta duk sun tabbata daga Annabi (SAW).
53. Amma abun da ya fi falala shi ne a tafi a bayanta.
54. Ya halatta a raka gawa a kan abun hawa da sharadin a kasance a baya, amma abun da ya fi falala shi ne a tafi a kafa.
55. Komawa a kan abun hawa bayan an riga an binne gawa wannan ba matsala a ciki.
56. Ɗaukan gawa a kan akori kura ko wata mota ta musamman da ake tanada don daukar gawa da masu rakiyar ta wannan bai halatta ba kwata-kwata saboda dalilai kamar haka:

1. Yana cikin al’adun kafirai, kuma a shari’a an hana mu koyi da su. 
2. Bidi’a ne a cikin ibada kuma ya saba wa sunna ta aiki, ita ce daukar gawa a hannu, duk abun da ya kasance haka ɓata ne bisa haɗuwar malamai.
3. Yana sarayar da manufar ɗaukan gawan da raka ta, shi ne tunatar da mutane lahira. 
4. Yana haifar da ƙarancin masu bin gawar da samun ladan hakan, saboda ba kowa ne yake da halin zuwa a motar ba. 
5. Ya saba da abun da aka sani na shari’a tsarkakakkiya mai sauki, na nisa daga shigowar sababbin ka’idoji, musamman a cikin abu mai hadari irin mutuwa. 
57. Tashi tsaye wa gawa shafaffen hukunci ne, kuma ya rabu gida biyu;
1. Tsayawar wanda yake zaune idan an zo za a wuce da ita.
2. Tsayawar wanda ya raka gawar idan aka isa kabari har zuwa a ajiye ta a ƙasa .
- Ana so wanda zai ɗauki gawa ya yi alwala.

Bayani a kan sallar janaza da binne gawa da ta'aziyya zai zo a wani rubutun

Daga Littafin "Masa'ilu ahkamil janaiz wabida'iha na Muhd Nasiruddinil Albani da Abubakar Al-anshawi ya tattara" 

Fassara: Mallam Bahaushe 18/10/2023

Comments